Kannywood
Kalli Hoton General BMB Tare Da Rahama Sadau Da Ya Jawo Cece-Kuce
Taurarin fina–finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB kenan tare da Rahama Sadau a wannan hoton inda ya dora hannu a kafadar Rahamar, sun dauki hotonne a lokacin da Bello ya ziyarci gurin daukar shiri Mati a Zazzau.
Bello ya saka hoton a dandalinshi na sada zumunta inda yace yasan wasu zasu yi kushe akan hoton amma su sani ko wane aiki ya dangantane da irin niyyar da aka nufeshi da ita.
Ya kara da cewa fim din Mati a Zazzau na musamman ne wanda zai nishadantar da ‘yan kallo sosai.
Saidai da dama wanda suka bayyana ra’ayoyinsu akan wannan hoton sun ce be dace ba.
Ga wasu daga cikin ra’ayoyin mutane akan hoton: