Kannywood
Kafi Gwanma Na Kwana Casa’in Bashi Da Lafiya
Jarumi Umar Yahaya Malumfashi Wanda Akafi Sani Da (Kafi Gwamna) A Shirin Kwana Casa’in. Yana Fama Da Rashin Lafiya, Inda Yake Neman Al’umma Su Tayashi Da Addu’a Na Neman Lafiya Daga Wajeb Ubangiji.
Jarumin Ya Shafe Lokaci Yana Fama Da Ciwon, Inda Tun Kwanakin Baya Aka Kwantar Dashi A Wani Asibiti, Yanzun Haka Jarumin Yana Kwnce A Wani Asibitin Kudi A Garin Kano, Inda Akace Yana Tsananin Fama Da Cuta.
Daga Bisani Ya Roki Al’ummar Musulmai Su Mishi Addu’ar Neman Lafiya, Domin Allah Ya Tashe Kafadunsa Ya Dawo Yaci Gaba Da Harkokinsa.
Muna Fatan Ubangiji Allah Ya Bashi Lafiya. Amin Summa Amin.