Labarai

Jirgin Saman Sojin Najeriya Ya Rikito A Kaduna.

Jirgin Saman Sojin Najeriya Ya Rikito A Kaduna.

Rahotanni sun ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

Al’ummar da ke kusa da hedikwatar cibiyar horas da matuka jiragen sama na sojin Najeriya da ke Mando a karamar hukumar Igabi suka shaida haka.

Har yanzu dai hukumar gudanarwar rundunar sojin saman Najeriya ba ta bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, sai dai mazauna yankin sun shaida cewa jirgin mai saukar ungulu ya yi hadari ne da sanyin safiyar Litinin a kauyen Taimi da ke kusa da Rigachikun.

Bayan afkuwar lamarin, an ce tawagar jami’an sojin sama daga cibiyar horaswar da kuma makarantar Flying 401 sun killace wurin da lamarin ya afku domin gudanar da ayyukan ceto da kuma binciken musabbabin hatsarin.

Back to top button
error: Content is protected !!