E News

Jerin Manyan Mata 10 Da Badaƙala Ta Dabaibaiye Kujerunsu

Jerin Manyan Mata 10 Da Badaƙala Ta Dabaibaiye Kujerunsu A Najeriya

Wasunsu zargin ne ya yi sanadin rabuwarsu da kujeru, wasu kuma bayan sun sauka ne, wasu kuma har yanzu tsuguno ba ta kare ba.

Ga wasu shahararru daga cikinsu:

1- Sadiya Umar-Farouq:

Sadiya Umar Farouq

Zargin karkatar da Naira biliyan 37 ta hannun wan dan kwangila, amma ta musanta sanin dan kwangilar ballantana mu’amala da shi.

2- Betta Edu:

Dr betta Edu

Bakalalar kudaden tallafin masara karfi daga hukumar kula da shirin, da kuma neman amfani da ofishin Akanta-Janar na Kasa wajen karkatar da miliyan 583 na tallafin na jihohi hudu zuwa asusun wata mata ta.

3- Halima Shehu:

Halima Shehu

An dakatar da Shugabar Hukumar ba da tallafin dogaro da kai (NSIP), kan tura kudaden gwamnati kimanin biliyan 44 zuwa asusun wasu mutane da hukumomi ba bisa ka’ida ba. Haima dai ta ce ta yi haka ne sakamakon umarni da matsin lamba daga ministar jinkai Bette Edu, amma ita tun da farko ba ta gamsu da hakan ba.

4- Muheeba Dankaka:

Muheeba Dankaka

Zargin badakalar karbar mili kudade daga hannun masu neman aiki a Hukumar Raba Daidai da kasa da ke karkashin shugabancinta. Muheeba dai ta musanta zargin har ta yi ransuwa a gaban kwamitin majalisar dokoki kasa cewa ba ta da hannu a ciki.

5- Pauline Tallen:

Pauline Tallen

Bayan zargin tsohuwar ministar harkokin mata, Paulin Tallen da karkatar da Naira biliyan biyu, kotu ta haramta mata rike mukamin gwamnati har sai ta janye kalamantan gami da ba ba da hakuri kan saboda ta kira hukuncin Babbar Kotun Jihar Adamawa da ta soke nasarar Aisha Dahiru Binani a zaben da takarar gwamnan jihar na APC a matsain hukuncin je-ka-na-yi-ka.

6- Hadiza Bala Usman:

Hadiza Bala Usman

An zargi tsohuwar Shugaban Hukumar Jiragen ruwa da badakalar biliyoyin kudade da ministan sufuri na lokacin Rotimi Amaechi ke mata, har ta kai an dakatar da ita. Hadizai dai ta a musanta zargin.

7- Kemi Adeosun:

Kemi Adeosun

Badakalar amfani da takardar shaidar wa kasa hidima ta bogi, wanda a dalilin haka Kemi Adeosun ta sauka daga kujerarta da ministar kudi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kemi ta ce ba ta a san cewa takardar ta bogi ba ce, domin an sama mata ne bisa wakilci.

8- Stella Oduah:

Stella Oduah

Zargin facaka da kuma karkatar da biliyoyin kudade sun dabaibaye tsohuwar ministar sufurin jiragen sama a zamanin shugaba Goodluck Jonathan, zargin da aka jima ana kai-komo tsakanin Stella Oduah da kuma hukumar EFCC. A karshe dai Oduah ta zama Sanata a zamanin magajin Jonathan Muhammadu Buhari.

9- Diezani Alison-Madueke:

Diezani

Bٍٍadakalar da aka shafe sama da shekaru 10 ana fafatawa da tsohuwar ministar man fetur, wadda ake zargi da wawure biliyoyin kudade. A halin da ake ciki Diezani ta tsere zuwa kasar Birtaniya inda a can ma take fuskantar shari’a.

10- Patricia Etteh:

Patricia Etteh

Shugabar Majalisar Dokoki Patrici Ette ta rasa kujerarta a sakamakon badakalar kudade da ake zargin ta da facaka da kudaden majalisar.

 

Back to top button
error: Content is protected !!