Jerin Aure-Auren Da Ayi A Cikin KannyWood Cikin 2023
Jarin Aure-Auren Da Ayi Su A Cikin Masana’antar KannyWood A Shekarar 2023.
Lahadi, 1 ga Janairu
Editan finafinai a Kannywood, Yakubu Hafizu Ɗandago, da Safiyya Sa’eed Mika’ilku, a masallacin D. O da ke Gwale a cikin Birnin Kano.
Asabar, 7 ga Janairu
Mai ɗaukar sauti a Kannywood, Bilal Muhammad Naseer (Lion) da Jamila Isah Muhammad, a gida mai lamba L. I 18, Fulani Road, kusa da Ramadan Hospital, unguwar Nassarawa, Kaduna. A kan sadaki N100,000.
Juma’a, 27 ga Janairu
Jarumin Kannywood, Adam Abdullahi Adam (Abale), da Maryam Faruq Saleh, a Masallacin Uhudu da ke Kano.
Asabar 4 ga Fabrairu
Mawaƙin Kannywood, Adamu Mohammed Turaki, da Hadiza Hassan Galadima, a fadar Sarki Oriye Rindre na Wamba, Jihar Nassarawa. A bias sadaki N400,000.
Juma’a, 10 ga Fabrairu
Mawaƙi a Kannywood, Izzuddeen M. Doko, da jarumar Kannywood, Khadija Yobe, a Masallacin Juma’a a unguwar Nassarawa da ke garin Damaturu, babban birnin Yobe.
Asabar, 4 ga Maris
Jarumin Kannywood, Tijjani Abdullahi (Asase), da Khadija Ɗahiru Mu’azu Kyalli, a masallacin Baballe Ila da ke unguwar Gyaɗi-Gyaɗi, Kano.
Juma’a, 17 ga Maris
Daraktan Kannywood, Kamal S. Alƙali, da jarumar Kannywood, Hauwa Shu’aibu Garba (Maama H.S.G.), a masallacin Juma’a da ke layi na 19 , Shagari Quarters, Kano.
Juma’a, 26 ga Mayu
Hafsat Muhammad Rabi’u (Ummi), ɗiyar furodusa kuma ɗan kasuwan finafinai a Kannywood, Alhaji Rabi’ Koli da Suraj Tijjani Suraj, a masallacin Sultan Bello da ke unguwar Sarki, Kaduna.
Juma’a, 16 ga Satumba
Rabi’atu Abdullahi Maikano, ɗiyar tsohon shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, Alhaji Abdullahi Maikano Usman, da Khamis Garba Gezawa, a masallacin Al-Mannar da ke unguwar Rimi, Kaduna. A kan sadaki N150,000.
Juma’a, 24 ga Nuwamba
Editan finafinai a Kannywood, Hafz Hamisu (SB) da Iƙilima Tasi’u, a masallacin Juma’a na Kabala Costain, Kaduna. A kan sadaki N150,000.
Juma’a, 29 ga Disamba
Daraktan Kannywood, Ibrahim Usman Muhammad da Ruƙayya Halliru Goma Ibrahim, a masallacin Juma’a na Malali, Kaduna. A kan sadaki N100,000.
Juma’a, 29 ga Disamba
Jarumi a Kannywood, Isma’il Ishaq Koli da Nasira Zakariyya Aliyu, a masallacin Juma’a na Govenment Collage, Kaduna. A kan sadaki N100,000.
Asabar, 30 ga Disamba
Jarumin Kannywood, Abdullahi Amdaz da Amina Umar Timta, a gidan sarkin Gwoza da ke kan Titin Gombale, kusa da makarantar Capital, Giwa Barrack, Maiduguri, Jihar Barno.
Daga Fimmagazine.com