Kannywood

Jarumin KannyWood Abdullahi Amdaz Ya Angwance

MashaAllah! Shahararren Jarumin KannyWood Abdullahi Amdaz (Excellency) Ya Angwance Da Sabuwar Amaryarsa.

Kwanakin Baya Mawakin Ya Bayyana Takardar Gayyatar Daurin Aurensa, Inda Ya Ya Wallafa A Shafukan Sada Zumunta,

Inda Ya Bayyana A Shafinsa Kamar Haka.

Alhamdulillah, Dukkan yabo da godiya sun Tabbata ga Allah wanda yasa akayi taron bikina lafiya, cikin Kwanciyar hankali da yalwar arziki, Allah ya sakawa duk wanda suka halarci tarukan da mukayi da alkairi, wanda suka aika mana da sakon fatan alkairi suma muna godiya Allah yabar zumunci.

Haka nan ina godiya ga duk wanda suka bani lokaci da gudunmawarsu ta kowacce irin siga Allah ya saka da alkairi.

Abdullahi Amdaz

An Daura Auren Shahararren Mawaki Da Jarumin Fina Finan Hausa Ne A Garin Maiduguri. Allah Ya Sanya Alkairi Kuma Ya Bada Zaman Lafiya.

 

Back to top button
error: Content is protected !!