Labarai
Jarumin Fina Finan India Ya Kashe Kansa
Ƴan sanda a Indiya sun ce sun iske ɗaya daga cikin fitattun jaruman Bollywood Sushant Singh Rajput a gidansa da ke Mumbai
Suna tunanin jarumin mai shekara 34 ya kashe kansa ne wanda aka ruwaito kafin mutuwarsa cewa yana fama da da matsalar damuwa.
Ya fito a fina-finai kamar Kai Po Che and M.S Dhoni — tarihin ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan kuriket a Indiya.
A kwanakin da suka gaba ne kuma aka isko gawar manajan jarumin Disha Salian a mace.
Abokan sana’arsa da kuma masoyansa da dama ne suka yi jimamin rashinsa a Twitter tare da yin ta’aziyya ga iyalinsa.