Jarumi Ali Nuhu Zai Tura Dansa Kasar Turai Yaje Ya Koyo Kwallon Kafa
Rahotanni sun bayyana cewa jarumi Ali Nuhu na shirin tura danshi Ahmad Ali Nuhu zuwa kasashen turai domin koyon kwallon kafa
Ali Nuhun ya bayyana cewa zai ware kudi ko nawa ne domin ganin dan nasa ya zama zakakuri a fannin kwallon kafa
Haka kuma jarumin yayi la’akari da yadda sana’ar kwallon kafar ta canjawa abokinsa Ahmad Musa rayuwa
Rahotanni masu tushe sun bayyana cewar jarumi Ali Nuhu ya ware makudan kudade wajen tura yaron sa Ahmad, zuwa kasashen turai don ya goge a fagen kwallon kafa.
Rahotanni sun bayyana cewar jarumi Ali Nuhu ya canja shawarar daya dauka na ganin yaron nasa ya zama babban jarumi a masanaantar Kannywood.
Haka kuma jarumin yayi duba da yadda sana’ar murza Kwallon kafa ta take canja mutun zuwa babban matsayi a duniya, har ila yau Ali Nuhu yana mai son ganin yaron sa ya zama gwarzo kamar abokin sa Ahmad Musa, na Super Eagles.
Har ila yau rahotan daya zo a boye ya ce Ali Nuhu, ya shirya ci gaba da narka manyan kudade har sai ya cimma burin sa.
Sai dai masu bayyana raayoyi sun duba cewar jarumi Ali Nuhu, yana mai kallon rayuwar abokin sa Ahmad Musa, da irin daular da kwallon kafa ta saka shi, nada nasaba da daukar matakin a kan yaron nasa.
Ya sami shawarwari da daurin gindi daga Dan wasa Ahmad Musa, kafin ya sami damar tura yaron nasa zuwa Turai.
Da farko dai Ali Nuhu, ya sanya yaron sa Ahmad a harkar Fina-finai, inda yaron ya fito a fina-finai da dama don har ya lashe lambobin Yabo.