Kannywood

Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Yanda Ya Hadu DaMatarsa Har Suka Fara Soyayya

 
Ali Nuhu shi ne mafi sanuwar jarumi a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood. Jarumin ya fara da fitowa a matsayin dan wasa shekaru 20 da suka wuce daga baya likkafa ta yi gaba ya zama darakta ya kuma zama furodusa, inda a halin yanzu ya zama wani jigo cikin jiga-jigan da na ji da kunnena wasu ‘yan masa’antar na cewa lalle kasancewarsu a masana’antar ne ke rike da gudanuwar masana’antar Kannywood.
Jaridar Daily Trust ta tattauna da jarumin Kannywood da Nollywood din, inda ta tambayin jarumin da ya lashe kambin gwarzanta da dama kan ya ma aka yi ya hadu da mai dakinsa, Hajiya Maimuna Ali Nuhu.
Ga Amsar da Ali ya bawa Daily Trust: “Muna cikin aiki a fagen shirin fim din WASILA a shekarar 2000, kawai sai ta zo ta wuce ta shiga cikin gidan da muke daukar fim din, cikin wasa sai na cewa abokan aikina Ishaq Sidi Ishaq da Hajara Usman, ni fa na ga matar da zan aura.
“Hakan ya sa aka yi mata magana har muka fara magana da ita a wannan rana kuma muka samu fahimta. Bayan kwanaki biyu, sai na bukaci furadusan fim din WASILA, Yakubu Lere da ya sake hada ni da ita. Haka kuwa aka yi, mun sake haduwa kuma nan take muka tsunduma cikin soyayyar juna.”
Da aka tambayi Ali kan yadda ya yi nasarar hada rike iyalinsa da kuma sana’arsa ta jarumin finafinai, sai ya kada baki ya ce: “A rayuwa duk abinda mutum zai yi tabbata cewa zai yi tasiri a kansa da iyalinsa. A saboda haka yana da matukar muhimmanci ya warewa aikinsa ko sana’arsa lokaci ta yadda ba a su shiga lokacin kulawa da iyalinsa ba.

“Sirrin zama da iyali lafiya a matsayin mutum na tauraro ko ma a kowane layi mutum ya tsinci kansa bai wuce rike gaskiya da amana ba, da nunawa iyali kauna da basu kulawa. Yana da matukar muhimmanci ka samar da wata dangantaka da a ta bawa mai dakinka da ‘ya’yanka damar zama manyan abokanka. Ka basu damarsu, ma’ana kar ka tursasa su akan fahimta ko tsarinka, sannan ka zama abokin shawararsu a koda yaushe ta yadda za ku kulla aminci da yarda da juna ta yadda za su iya fada maka damuwarsu da farin cikinsu a kowane lokaci.
“Yana da matukar kyau ka karanci matarka da ‘ya’yanka, ta yadda za ka iya gane damuwarsu da nishadinsu ta yadda za ka shigo a yayin damuwa ka karfafe su, a yayin nishadi kuma a yi da kai.”
Ali Nuhu ya bayyana yawaitar mace-macen auren da ya addabi al’umma a matsayin rashin sauke hakki da wasu mazaje ke gaza yi da kuma mayar da mata ababen kare sha’awarsu.
Ali Nuhu ya bayyana mai dakinsa, Maimuna a matsayin wata jigo ta samun nasarorinsa da cikar burinsa. “Ta fahimci sana’ata, kuma tana bani tallafi wajen gudanar da sana’ata cikin kwanciyar hankali.
“Maimuna, uwa yanzu ta dauki nauyin finafinai har guda uku: Madubin Dubawa, Son Mai So da kuma Janjani.
“Duk da yanayin aikina da ya kansa lokuta da dama bana samun kasancewa da iyalina, nakan samu lokaci na debe su mu fita hutu wata kasa don na fanshe musu lokutan da suka kwashe ba tare da ni ba.”
Ali Nuhu ya bayyana zuwa dauko ‘ya’yansa daga makaranta a matsayin bangaren da ya fi burge shi a matsayinsa na uba. ” ‘Ya’yana, Fatima da Ahmad, nishadina ne,” ya fada cikin murmushi.
Back to top button
error: Content is protected !!