Kannywood

Jarumi Adam Zango Ya Goge Wanda Yake Bi A Instagram

Jarumi, Adam Zango wanda tauraruwar sa take haskawa a cikkin jerin jaruman masana’antar Kannywood, ya daina bin dukannin abokan sa na shafin sada zumunta na Instagram wato (unfollow) abun da ya jawo ce-ce-kuce a wurin mabuya shafukan sada zumuntar na Instagram.

A shekarar da ta gabata ne dai jarumin Adam Zango, ya fito ya bayyanawa duniya cewar ya fita daga masana’antar Kannywood saboda wasu dalilai na kashin kansa.

Sai dai tun a lokacin ne mutane da dama sun yi tunanin kawai ya fada ne bazai iya aikatawa ba, domin wasu sukan yi ikrarin sun fita daga baya kuma su dawo a ci gaba da damawa dasu, musamman da dai saboda furucin ne ya zo ne lokacin da ya ke tsaka da tashe kuma tauraruwarsa ta na kan haskawa. Sai dai kuma abin mamakin shi ne yadda ya ke kara nisanta kansa da masana’antar da kuma mutanen cikinta.

A cikin ‘yan kwanakin nan Jarumin ya kange (blocking) wasu daga ganin abubuwan da ya ke sa wa a shafukan sa na soshiyal midiya. Wanna mataki ya fara faruwa ne tun a lokacin da hukumar tace fina-finai ta umarci kowa sai yazo an tantance shi wanda an tabbatar da cewa duk wanda baiyi rigista ba sai dai ya bar harkar fim a garin Kano baki daya, wanda wasu ke zargin wasu Jarumai da a ke ganin shafaffu da mai ke yin bi ta da kulli ga Adam Zango.

Wannan mataki dai shi ne abun da a ke zargin hakan fusata Jarumi har ya Ali shi ga Jawabin komawa Kaduna da yin duk wasu harkokin san na yin fim. Daga baya kuma jarumin ya tattara gaba daya da iyalansa ya koma jihar Legas da zama da kuma ci gaba da harkokin kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Kwatsam a wannan mako sai ga shafin Adam Zango ya nuna cewa ya daina bibiyar abokan sa na dandalin sada zumunta wanda a ke cewa unfollowing. Hakan ya kawo ce-ce-kuce inda wasu su ke ganin ya burgesu wasu kuwa ya na ganin hakan ba daidai ba ne, wasu kuwa ko a jikinsu ‘wai an tsikari kakkausa’.

Ga dai irin kalaman da wasu daga cikin mabiya shafin instgram na jarimin abun da su ke cewa kamar haka:

Sirrin_arewa ya ce “ko me ya yi wallahi ba za muyi unfollow ba saboda muna son shi”.

Ummita _1700: “choice …. let’s respect that biko”

Real Khalid exclusive ya ce “to masu7 haddasa fitina”.

Arc sunusi baba ya ce “wallahi ya birgeni sai yanzu na na fara following dinshi”.

Bashir 6388 cewa ya yi” mugun nufin sa ne kawai ba wani abu ba “Naziru solari ya ce “girman kai ke nan, ai bai isa ya ce ba wanda ya fishi ba ko kuma babu wanda ya ke birgeshi”.

Abin tambayar a nan shi ne ko menene dalilin da ya sa jarumin ya daina bin kowa a shafin sa wanda ya hada har da matarsa da sauran shakikan abokansa da ba su da alaka da Kannywood?

Wannan dalili yasa majiyar mu ta so jin ta bakin jarumin, sai dai hakan ya ci tura sakamakon kasa samun layukan wayarsa da mu ka yi, amma za mu ci gaba da gwadawa ko hakar mu za ta cimma ruwa.

Daga Nothflix

Back to top button
error: Content is protected !!