Kannywood

Jarumi Adam A. Zango ya koma harkokinsa Kudancin kasar nan

Sanannen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya shaida wa Aminiya cewa zuwa yanzu ya koma birnin Legas da harkokinsa.

Jarumin ya ce, Ya koma can ne don bunkasa harkokinsa a kan yadda ya tsaya Arewa, “komawa ta Legas kamar wanda ya yi makarantar sakandare ne idan yana son cigaba da karatunsa sai ya nufi jami’a, wannan shi ne abinda nayi”.

Zango ya kara da cewa, irin karan tsanar da abokan sana’arsa suka aza masa yana cikin dalilinsa na yin kaura zuwa Legas.

Sanannen abu ne rikice-rikicen da suka taru suka yi katutu a masana’antar fina-finan hausar.

Idan zamu tuna, a kwanakin baya jarumi Adam A. Zango ya bayyana ficewarsa daga masana’antar
Kannywood. Hakan ya tabbata ne kuwa ta yadda jarumin ya ki halartar rijistar ‘yan masana’antar da hukumar tace fina-finai ta yi.

Tuni jarumin ya wallafa fitarsa daga masana’antar a shafinsa na Instagram. Bayan nan kuwa, ya fito ya bayyanawa jama’a cewa zai cigaba da yin fina-finansa amma za a iya kallonsu ne kai tsaye ta kafar YouTube.

Hakanne kuwa ya faru, domin jarumin ya shirya fina-finansa inda ya wallafa su a kafar YouTube don cigaba da nishadantarwa tare da ilimantar da masoyansa.

source

Back to top button
error: Content is protected !!