Kannywood

Jarumar Fim Da Ta Sha tabar W Da Shafin Bible Ta Ce a Shirye take ta yayyaga Qur’ani idan aka bata

 Fitacciyar jarumar fina-finan Kudancin Najeriya Etinosa Idumedia ta sha zagi a wajen mutane bayan ta wallafa wani sabon bidiyo a shafinta na Instagram da ya jawo kace-nace

Jarumar dai ta wallafa wani bidiyo ne da aka nuno ta tana shan tabar wiwi da shafin littafin Bible, sannan ta bayyana cewa babu komai a jikin shafin sai karya

Jarumar dai dama ba bakuwa bace wajen jawo kace-nace a shafukan sada zumunta, domin kuwa kwanakin baya ta wallafa wani bidiyonta tsirara a shafinta na Instagram da ya jawo kace-nace

Fitacciyar jarumar fim ta kudancin Najeriya Etinosa Idemudia ta sha zagi daga wajen masoyanta bayan ta wulakanta litaffin Bible sannan kuma ta sha alwashin wulakanta Al-Qur’ani mai girma idan aka bata a wani sabon bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa.

A bidiyon, jarumar wacce take haifaffiyar garin Warri ta yaga wani shafi a jikin littafin Bible din inda tayi amfani da shi ta sha tabar wiwi, sannan kuma tace duka karya ce a jikin shafin.

Sai dai kuma wasu daga cikin masoyanta sun nemi da idan har ta isa ta gwada yin wannan cin mutunci da ta yiwa Bible akan Al-Qur’ani mai girma, cikin gaggawa kuwa jarumar ta maida musu martani kamar haka: “Ina bukatar littafin Qur’ani yanzu-yanzu, wace irin magana ce wannan, ku bani Qur’ani yanzu zanyi kaca-kaca da shi a cikin dakika biyu. Su waye ku da har zaku kalubalance da wasu littattafai guda biyu?”

To sai dai kuma wannan martani da jarumar ta bayar ya jawo mata zage-zage da Allah wadai a dukkanin bangarori guda biyu na Musulmai da Kirista.

Etinosa ba bakuwa bace wajen jawo kace-nace a shafukan sada zumunta na zamani domin kuwa a kwanakin baya an sha fama da ita bayan ta wallafa wani bidiyo nata tsirara a shafinta na Instagram.

Back to top button
error: Content is protected !!