Jaruman KannyWood Da Allah Ya Albarkace Su Da Haihuwa A 2023
MashaAllah! Wasu Daga Cikin Jaruman KannyWood Da Allah Ya AlbarKace Su Da Haihuwa A Shekarar 2023 Data Gabata.
Litinin, 23 ga Janairu
Allah ya azurta jarumi a Kannywood, Malam Aminu Mirror da ‘ya mace. Matar sa Malama Zulaihat ta haihu a gidan sa da ke Zariya.
Lahadi, 29 ga Janairu
Allah ya albarkaci tsohuwar jarumar Kannywood, Maryam Musa Waziri, da ɗa namiji. Maryam ta haihu a wani asibiti a Kaduna. An raɗa wa jaririn suna Muhammad (Fadeel).
Litinin, 9 Oktoba
Allah ya azurta jarumin Kannywood, Yusuf Muhammad Abdullahi (Sasen) da ɗa namiji. Ameena Zakari Yusuf ta haihu asibitin MGK, daura da asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano a birnin Kano. An raɗa wa jariri Muhammad Auwal.
Cikin Watan Nuwamba Allah Ya Albarkaci Jarumi Adamu Abdullahi Wato (Daddy Hikima Abale) Da Samun Karuwar Diya Mace.
Lahadi, 10 ga Disamba
Allah ya albarkaci tsohuwar jarumar Kannywood Malama Zulaihat Ɗalhat da jarumin Kannywood Shu’aibu Idris Lilisco da ‘ya mace. Zulaihat ta haihu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano. An raɗa wa jaririya Halima.
Kamal Alkali Da Matarsa Tsohuwar Jaruma A Masana’antar KannyWood Suma Sun Sami Qaruwa, Inda Su Sami Diya Mace. Muna Fatan Allah Ya Raya Musu Kuma Ya SanyawaA Abin Da’a Samu AlbarKa.
A Cikin Shekarar Ne Allah Ya AlbarKaci Jaruma Rahama MK. Wacce Akafi Sani Da Hajjiya Rabi Bawa Mai Kada Ta Cikin Shirin Kwana Casa’in Samun Qaruwa. Inda Itama Ta Samu Diyarta Mace.