Kannywood

Jaruman Kannywood 11 Da Suke Fi Yawan Mabiya A Shafin Instagram

Dandalin sada zumunta na Instagram shi ne shafin da jarumai da kuma masu hurda da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sukafi maida hankali akan sa

Dukkan wani mutum mai neman gulma ko tsokaci akan masana’antar Kannywood da jarumanta, to wajen da zai fara tunkara shine shafinsu na Instagram domin a nan ne mutum zai ga dukkanin wainar da ake toyawa.

A daidai lokacin da ya rage saura kwana daya kacal mu fita daga shekarar 2019, Jaridar Hausa ta binciko muku jerin manyan jaruman da suke amfani da dandalin na Instagram, inda muka samo muku jarumai 11 da suke da yawan mabiya a masana’antar.

1. Rahama Sadau

2. Hadiza Gabon

Rahama Sadau ita ce jarumar da tafi kowa mabiya a dandalin Instagram, inda take da mabiya kimanin miliyan daya da dubu dari bakwai (1.7m).

Hadiza Gabon ita ce ke biyewa Rahama Sadau, inds take da yawan mabiya miliyan daya da dubu dari biyar (1.5m).

3. Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi na da mabiya miliyan daya da dubu dari uku (1.3m) a dandalin Instagram.

4. Ali Nuhu

Haka shima jarumi Ali Nuhu yana da mabiya kusan daya dana jaruma Nafisa Abdullahi, inda shima yake da mabiya miliyan daya da dubu dari uku (1.3m).

5. Adam A Zango

Jarumi Adam A Zango shine wanda yake bin jarumi Ali Nuhu, inda yake da mabiya miliyan daya da dubu dari biyu (1.2m).

6. Fati Washa

Haka ita ma jaruma Fati Washa tana da mabiya miliyan daya da dubu dari biyu (1.2m) kamar dai jarumi Adam A Zango.

7. Maryam Booth

Jaruma Maryam Booth ita ma yawan mabiyanta ya kai miliyan daya da dubu dari biyu (1.2m).

8. Hafsat Idris

Jaruma Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya ita ma tana da mabiya miliyan daya da dubu dari biyu (1.2m).

9. Sadiq Sani Sadiq

Jarumin wanda yayi fice wajen fitowa a kowanne irin mataki da aka bashi yana da mabiya miliyan daya (1m).

10. Maryam Yahya

Jarumar Maryam Yahya jaruma ce da tauraruwarta tafi haskawa a shekarar nan ta 2019, inda ita ma take da mabiya miliyan daya (1m).

11. Aysha Humaira

Ita dama jaruma Aysha Humaira ta jima da yin fice a dandalin Instagram kafin daga baya ta fara fitowa a shirin fim na Kannywood, jarumar na da mabiya miliyan daya (1m) a dandalin.

Back to top button
error: Content is protected !!