Kannywood

Jarumai Mata Da Suyi Aure Lokacin Tauraronsu Na Haskawa

Bayani Game Da Jarumai Mata Da Suyi Aure A Lokacin Da Tauraruwarsu Take Tsaka Da Haskawa, Wadannan Jaruman Dai Kamar Yadda Kowa Ya Sani Sun Za6i Suyi Aure Ne Suje Dakin Mijinsu A Lokacin Da Ake Yayin Su.

Da Yawa Wasu Jaruman Sukanyi Aure Ne Bayan Tauraransu Ya Fara Ko Kuma Ya Gama Dusashewa, Sai Dai Su Wadannan Nasu Ra.ayin Daban Dana Irin Wadancan, Kamar Auren Maryam Malika Tayi Aure Ne A Lokacin Da Kowa Ke Son Yaga Jarumar A Cikin Fim.

Ita Maryam Wazeery Kuma Ta Dade A Masana’antar KannyWood Sai Dai Kuma Ba Kowa Yasan Jarumar Ba, Sai Da Aka Fara Nuna Shirin Labarina Series Inda Nan Ne Jarumar Tayi Shuhura, A Dai Dai Lokacin Da Tauraronta Yake Kan Haskawa Sai Ta Shiga Dakin Mijinta.

Marigayya Balaraba Kaduna Itama ‘Yar Uwa Ce Ga Maryam Malika Itama Kafin Aurenta Da Shu’aibu Lawal (Kumurci) Tana Kan Ganiyarta Ne A Masana’antar KannyWood, Sai Ta Zabi Tayi Aure Kan Fina Finai.

Jaruma Rahma MK, Wacce Akafi Sani Hajiya Rabi Bawa Mai Kada Itama Jaruma Ce Wacce Ta Juma A Cikin Masana’antar, Sai Dai Batayi Wani Suna Ba. Amma Kuma Zuwan Shiri Mai Dogon Zango Na “Kwana Casa’in” Shine Dalilin Da Yasa Tauraruwar Jarumar Ta Haska. Itama Daga Baya Ta Za6i Aure Akan Fim.

Akwai Jaruma Zahra Diamond Wacce Itama Bata Dade Dayin Aure Ba Wacce Itama Tana Kan Ganiyarta, Sai Dai Daga Bayan Nan Muna Jin Labarin Cewa Auren Jarumar Ya Mutu.

 

Back to top button
error: Content is protected !!