Jaruma Zeepreety tana fama Da rashin lafiya
Matar jarumin Adam A. Zango ta wallafa wani rubutu a shafinta kan rashin lafiyar jaruma Zee Preety wanda ya daga wa mutane hankali
– Ina ma zan iya miki magana, ina ma zaki iya bani amsar sakona, ina ma zan iya ganinki, Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, cewar Safiya Umar Chalawa
Wannan rubutun kuwa ya tashi hankulan masoyan Zee Preety din inda suka dinga korafin cewa wannan kalaman ga mamata ake fadinsu
Safiya Umar Chalawa, matar fitaccen jarumi Adam A. Zango tayi wani rubutu a shafinta na Instagram wanda ya ja hankalin mutane game da rashin lafiyar kawar ta jaruma Zee Preety.
Kowa dai ya san irin aminci mai karfi dake tsakanin jaruma Zee Preety da matar ubangidanta Adam A. Zango Wato Safiyya Umar Chalawa. Don suna yawan wallafa hotunan juna a shafukansu gami da yiwa juna fatan alkhari. Wanda ko a kwanakin baya da matar Adam Zango tayi bikin zagayowar ranar haihuwarta, jaruma Zee Preety ta sa an gwangwajeta da waka don taya ta murna.
Ga dukkan alamu, jaruma Zee Preety na fama da matsananciyar rashin lafiya, wanda hakan ya tashi hankalin kawartata har tayi wani rubutu a shafinta wanda ya kada hanjin mutane.
Safiyya ta wallafa hoton Zee Preety inda ta wallafa cewa
“ina ma zan iya miki magana, ina ma zaki iya bani amsar sakona, ina ma zan iya ganinki, Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Wallahi ina tsananin kewarki kamar hauka. Ya Allah ka ba Zee Preety lafiya, ya Allah ka tashi kafadunta, ya kuma bata lafiya alfarmar Annabin rahama.”
Wannan rubutun kuwa ya tashi hankulan masoyan Zee Preety din inda suka dinga korafin cewa wannan kalaman ga mamata ake fadinsu ba ga mara lafiya ba don ta kada musu hanjin ciki.
A zahirin gaskiya dai duk wanda ya karanta jawabin nata, kafin ya kai karshe zuciyarshi zata tsinke, sai daga karshe da tayi mata fatan samun lafiya aka gane ba mutuwa tayi ba.
Daga Shafin Netnaija