Jaruma Rashida Mai Sa’a Zata Shiga Daga Ciki
Katin Gayyatar Auren Jarumar KannyWood Rashida Mai Sa’a, Inda Zatayi WUFF! Da Wani.
A Ranar Asabar Mai Zuwa, 11 Ga Nuwamba 2023 Za a Ɗaura Auren Jarumar Kannywood ɗin Nan Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a Tare Da Masoyin Ta, Aliyu Adamu (Sardaunan Matasan Goza).
Za’a Ɗaura Auren Ne A Gidan Mahaifin Ta Da Ke Layin Malam Bello A Unguwar Daurawa, Kusa Da Titin Maiduguri, A Cikin Garin Kano, Da Misalin Ƙarfe 9 Na Safe.

Sanarwar Daurin Auren Tazo Ma ‘Yan Fim Da Bazata, Domin Kuwa Ba Kowa Bane Ya San Da Maganar Na Auren Nata.
Tuni Dai Jama’a Daga Ciki Da Wajen Masana’antar Shirya Fina-finai Su Ka Shiga Yi Wa Amarya Rashida Fatan Alheri Tare Da Taya Ta Murna Game Da Wannan Abin Alkairi Da Farin Cikin Daya Sameta.
Allah Yasanya Alkairi Allah Ya Basu Zaman Lafiya.







