Kannywood

Jaruma Rahama Sadau ta bude gidan shan shisha a Kaduna

Fitacciyar jarumar Kannywood , Rahama Sadau ta bude gidan kwalliya mai suna ‘ Sadau Home ’ a Kaduna.

Tun farko dai jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa zata bude sabon waje mai suna ‘Sadau Home’ a Kaduna.

Ta kira wajen da ‘wurin da ya kamata ka je a Kaduna.’ Jarumar dai ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta karo na 26.

A Sadau Home, akwai bangaren shan Shisha wanda ya ja hankulan ‘yan Arewacin kasar nan .

Kamar yadda ma’anar Shisha take, kalma ce a harshen larabci mai nufi da kwararo na kona taba. Wannan bangaren na shan Shisha kuwa, ya ja hankulan sanannun ‘manyan yara’ na kasar nan.

A cikin kwanakin nan, da yawa daga cikin taurarin masana’antar sun bazama duniyar kasuwanci. Sun hada da Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Sani Danja da sauransu.

A yayin tsokaci a kan bude wajen shan Shisha da Rahama Sadau ta yi, Muhsin Ibrahim, malami ne a jami’ar Cologne da ke kasar Jamus, ya ce: “Lokaci ya yi da zamu gane cewa, jaruma Rahama Sadau ba ta damu da abinda mutane ke cewa a kanta ba.

Duk yadda muka dauka wajen shan Shisha; dai-dai ko akasin hakan, matukar zai amfaneta bata damu ba. Shisha dai ta matasa ce, kuma al’ada ce ta birni. Wajen shan Shishar Sadau ta matasa ce.”

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng
Back to top button