Jaruma Maryam Yahaya Ta Bayyana Dalilin Da Ya Hanata Yin Aure
Shahararriyar jarumar Kannywood, Marayam Yahaya ta bayyana dalilin da yasa bata yi aure ba har yanzu
A cewar jarumar, rashin mijin aure ne ya kawo mata wannan tsaikon
A kwanakin baya ne Abubakar Bashir Maishadda ya bayyana cewa, Allah ne bai yi aurensa da jarumar ba
Shahararriyar jarumar fina-finan hausa, Maryam Yahaya ta bayyana dalilin da ya hanata aure.
Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar da tayi da gidan rediyo na Freedom dake Kano.
Jarumar tace: “Da aure da mutuwa duk lokaci ne, idan lokaci kuwa yayi ai zan daga. Baabu mijin ne, hakan ne ya hanani auren. Ku fito ku aureni, kunsan aure maza yanzu wuya suke.”
A kwankin baya ne dai hotuna suka dinga yawo a kafafen sada zumunta ana cewa, an kasa Maryam Yahaya don kuwa saurayinta Maishadda zai angwance da matashiyar jaruma Hassana Muhammad.