Kannywood

Jaruma Hadiza Gabon Ta Zagi Wani Mabiyinta AkanYa kirata Da Tsohuwa

Sarakan magana suna cewa idan kasan ta fada baka san ta mayarwa ba


Mun samo labarin yadda fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Hadiza Gabon ta dinga sirfawa wani mutumi zagi saboda ya kira ta da tsohuwa
Mutane da yawa sun goyi bayan abinda jarumar tayi, inda wasu kuma suke ganin abinda tayi din bai dace ba
Kwanan nan ne dai fitacciyar jarumar fina-finan Hausan nan Hadiza Gabon ta dora wani sabon hotonta da ta dauka akan shafin sada zumunta na Istagram, domin masoyanta da abokan arziki su kalla.
Kwatsam sai aka jiyo wani daga cikin masu binta shafin nata yayi rubutu a kasan hoton nata a turance kamar haka, inda ya ce: “You looked so beautiful but you are old” ma’ana “Kinyi kyau sai dai fa amma kin tsufa.”



Hakanne ya tunzura fitacciyar jarumar ta maida masa martani a turance kamar haka: “I am your mother’s mate!” ma’ana “Ni sa’ar uwarka ce!”
Hakan shine yadda sarakan magana suke cewa idan kasan na fada baka san na mayarwa ba.
Sai dai kuma bayan jarumar ta mayarwa da mutumin martanin, wasu daga cikin masoyanta sun dan yi korafi akan furucin nata, inda suke ganin abinda ta fada din bai kamata ba. Yayin da wasu kuma suke ganin abinda ta yi din yayi daidai.
Back to top button
error: Content is protected !!