Kannywood

Jaruma Fati Muhammad Ta Yi kira Da babbar murya Ga Yan Matan Kannywood masu Tasowa

Fitacciyar jaruma Fatima Muhammad wacce a ka dade ana damawa da ita a masana’antar kannywood da duk wata duniyar fina-finai hausa, Jarumar da ta fi kowacce jaruma fice, farin jini da kuma yawan masoya tayi kira ga sauran jarumai mata yan uwanta masu tasowa da su riqa Kare mutuncin kansu sannan su San irin mazajen da zasu ke mu’amala Northflix na ruwaito.

Fati Muhammad ta qara da cewa tana kiran jaruman mata da su cire girman kai ga masoya su ajiye shi a gefe domin ba komai cikin girman kai sai jahilci da kuma shedanci sannan kuma babu inda zai kai mutum sai halaka tare da ragewa mutum mutuncin shi da kuma kima.

Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da suke wata tattaunawa da wakilin mu, ta fadi hakan ne a matsayin shawara ga jarumai mata masu tasowa a lokacin da wakilinmu ya tambayeta ga me da rayuwar Kannywood a yanzu da kuma wane shawara zata bawa jaruman.

Jarumar ta qara da cewa Allahu subhanahu wataala shi ya halacci aure kuma ya halicci saki, duk da cewar mutuwar aure bashi da kyau amma Allah ya halatta shi, sannan duk cecekucen da ake kan cewa idan munyi aure bama zama muma ba’a son ranmu ba ko son zuciyarmu bane ace mun raya sunnar manzo sannan ace yau wance ta fito ko wane ya saki matarsa.

Sai dai kuma idan mutane za suyi mana uzuri su kuma gane ba’a kan ‘yan fim kadai aure ke mutuwa a duniya ba, akwai mutane da dama da auren su yake mutuwa, wani gidan idan ka shiga sai ka tarar da zaurawa biyu uku koma fiye da haka, duniya ba ta Sanar ba shiyasa babu wanda na ya san da zaman su. Kuma shiyasa babu wanda ya ankara da haka sai dai mu.

jarumar ta koka da yadda maza da dama suke yi wa ‘yan fim auren sha’awa wanda shine babban dalilin mutuwar auren su, a cewarta wasu mazan sukan kashe kudi masu yawan gaske don ganin sun auro ‘yar fim kuma da sun gama biyan bukatunsu sai su sake mu. da zaran sun sake mu ba’a duba cewa sun zalince mu sun sake mu sai ace ai dama baza ta zauna ba, bata son ta zauna ta amince har ya kaishi gaban iyayen ta?.

Yawancin jarumai mata idan aurensu ya mutu suna dawowa harkar fim, duk da kema za’a ce a kwanakin baya bayan mutuwar aurenki na farko kin dawo fim sai daga baya kika fice kika koma siyasa, ko meye dalilin da ya saka kika zabi siyasa akan harkar fim? Wannan itace tambayar da wakilinmu yayi mata

Jarumar tace “akwai mata da yawa wadanda suke da ayyukan yi kafin suyi aure, wasu aikin banki suke wasu na aikin asibiti, wataqila idan sunyi auren wani dalili ya saka su bar aikin nasu, amma idan auren su ya mutu su kanyi shawarar komawa makaranta ko su koma bikin aikin su.

To haka ne ma a kannywood, a nan aka sanmu nanne wajen sana’ar mu , kuma a nan din wataqila Allah ya sake hada mun da wani mijin muyi aure,.

Sannan kuma ni a bangare na lokacin da na dawo daga Landan na dawo fim, sannan daga baya na zo na bari, ba wai haka kawai na bari ba, na bari ne na bawa ‘ yan baya dama suma, domin a rayuwa bazai yiwu kaci lokacinka ka kuma ci na wani ba. Maganar shiga siyasa kuma ita rayuwa tun kana cikin mahaifiyarka Allah yake kaddara maka rayuwarka, ban taba tunanin zanyi siyasa ba amma kamar da wasa na fara kuma da Allah ya bani nasibi sai abun ya karbe ni da Allah ya rubuta a tarihin Fati Muhd zatayi siyasa.

wakilinmu ya tambayi Fati ko tana da sha’awar sake yin aure yanzu?

“Ina da sha’awar yin aure gaskiya domin duk dan aure bazai qi aure ba, aure shi ya haifeni don haka bazan qi shi ba, duk da ban rasa manema ba amma Ina nan Ina roqon zabin Allah saboda kar na bi son zuciya.

Fatana kawai mutum ya kasance mai tsoron Allah wanda zai kula dani ya kuma kula da maraici na ba wanda kwana biyu zan samu matsala dashi ba tun ana ganin hakurinka har aga gazawarka ba. Kuma kullum Ina addu’a Allah ya hada ni da miji na gari bama ni kadai ba duk wata mace da bata da aure”. Cewar Fati Muhammad

Back to top button
error: Content is protected !!