Kannywood

Jaruma Fati KK Ta Bayyana Sabon Angonta

Tsohuwar Jarumar KannyWood Fati KK, Ta Bayyana Sabon Angonta Da Tayi WUFF! Dashi!!! A Kwanakin Baya Ne Ayi Yayin WUFF, Inda Mace Mai Babban Shekaru Zata Nemi Dan Matashin Namiji Ko Kuma Namiji Mai Manyan Shekaru Ya Nemi Yarinya Mai Karamin Shekaru Su Aure Juna.

Daga Wancan Lokacin Anyi Tunanin Wannan Yayin Na WUFF Ya Wuce, Sai Kuma Yanzun Yayin Ya Shigo Masana’antar KannyWood, Inda Wasu Daga Cikin Jaruman KannyWood Kamar Irin Su Rashida Adamu (Mai Sa’a) Ta Dakko Yaron Da Ta Bashi Shekaru Masu Yawa, Ta Aureshi Inda Suketa Cin Duniyarsu Da Tsinke, Haka Ayi Tsakanin Tsohuwar Jaruma Fati KK, Inta Itama Allah Ya Bata Nata Dan Matashin,

Itama Tsohuwar Shahararriyar Jaruma Farida Jalal, Wacce Ta Koma Wakokin Yabon Ma’aiki SAW, Itama Tayi WUFF Da Wani Dan Matashi Wanda Ake Tunanin Shekarunta Ya Dara Nasa.

Dukansu Dai Muna Musu Fatan Allah Ya AlbarKaci Tarayyar Nasu, Kuma Allah Ya Karo Wasu Wanda Suma Zasu Shiga Daga Ciki.

Back to top button
error: Content is protected !!