Kannywood

Jaruma Farida Jalal Ta Dawo HarKar Film

Tsohuwar jaruma Farida Jalal ta yiwa masana’antar Kannywood kome bayan barin masana’antar na lokaci mai tsawo

An yi magana da jarumar baki da baki inda ta bayyana cewa tabbas ta dawo harkar fim, har ma ta bayyana sunan wani sabon fim na ta da zai fito kwanan nan

Jarumar ta bayyana cewa tana so masoyanta su cigaba da bibiyarta kamar yadda suke yi a da can lokacin da tauraruwarta ke haskawa

Ga mutanen da suka dade suna bibiyar fina-finan Hausa na Kannywood tun tsawon lokaci da ya shude, jaruma Farida Jalal ba bakuwa bace a gurin su sai dai ga sababbin zasu iya ganin ta a matsayin bakuwar fuska duba da irin tsawon lokacin da aka kwashe ba tare da anga fuskar jarumar ko anji duriyarta ba.

Kwatsam a ‘yan kwanakin nan sai aka fara ganin jarumar jefi-jefi a guraren daukar fim wanda ke nuni da cewar jarumar ta yiwa masana’antar kome, hakan yasa wani mai sharhi kan al’amuran masana’antar yayi sharhi kan tafiya da dawowar jarumar inda ya fara da cewa:

“Shin Farida Jalal ta dawo fim ne? Da alama dai yanzu yayin dawowar tsofaffin jarumai a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood ake yi, wadanda suka ci zamanin su a baya, kuma a yanzu ma suke kara dawowa da tunanin za su kara cin duniyar su da tsinke ba tare da la’akari da yadda masana’antar take ba a halin yanzu.

“Farida Jalal tana cikin tsofaffin jarumai da suka ci zamanin su a baya wadda a cikin shekarar 2002 kusan babu wata jaruma da take tashe kamar Farida Jalal, kafin daga baya harkar ta ajiye ta, ko da yake za a iya cewa hayaniyar Hiyana ce ta taba ta a shekarar 2007 lokacin da aka kori wasu daga cikin ‘yan fim cikin su kuwa har da Farida Jalal, tun daga nan dai aka daina ganin ta a cikin harkar fim, sai dai daga baya ne ta auri wani malami in da har suka samu haihuwa tsakanin su, amma dai daga baya auren ya mutu don haka sai ta koma gida Katsina da zama.

“A yanzu dai za a iya cewa Farida Jalal ta dawo cikin ‘yan fim don kuwa jefi-jefi ana ganin ta a wajen daukar fim, kuma a kwanan nan an yi wani aikin fim da ita a Kano, akwai kuma wakoki da za su fito nan gaba kadan wadanda ta fito a cikin su.

“Abin da mutane suka dade suna tambaya shine wai me ya sa ‘yan fim komai dadewar su da barin harkar fim duk lokacin da suka samu dama sai su dawo? Shin wani asiri ake yi musu ko kuma harkar tana shiga jini ne?”

Kwatsam kuma sai muka ci karo da wata tattauna da aka yi da jarumar inda da bakin ta tabbatar da dawowar ta bakin aiki ta inda take cewa:

“Akwai sababbin fina-finanta da suke shirin fitowa, saboda haka tana so masoyanta su zuba ido, ciki kuwa hadda wani mai suna ‘Kallabin Kishiya’.”

Shin ya kuke kallon wannan kome na wannan jaruma ga masana’antar Kannywood shin kuna ganin cewa za ta kara yin sharafi kamar yadda tayi a baya ko kuwa dai ta makaro?

Back to top button
error: Content is protected !!