Jami’an DSS A Kano Sun Farma Masu Garkuwar Da Mahaifiyar Rarara
Jami’an DSS A Kano Sun Farma Masu Garkuwar Da Mahaifiyar Rarara Lokacin Da Suke Tsaka Da Kasafta Kudin Fansa, Sun kashe Kuda Sun Kama Guda Yayin Da Suka Ƙwata Sama Da Naira Miliyan 25
Rahotanni sun ce zaratan jami’an hukumar tsaro ta DSS da ke aiki a ofishin hukumar na Kano ne bayan sun tattara bayan sirri suka farwa gaggan ‘yan garkuwar da suka yi garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara, a yankin Maƙarfi lokacin da suke tsaka da kasafta kuɗin fansar da suka ƙarɓa, inda jami’an hukumar suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar kuma nan take suka hallaka ɗaya daga cikin ‘yan bindigar mai suna Bature, yayin da a yanzu haka suna tsare da ɗaya mai suna Hamisu Tukur, wanda ya sami raunin bindiga a musayar wutar.
A rahoton Jaridar Dailytrust ta ce jami’an na DSS sun kuma yi nasarar gano Naira miliyan 25 da dubu 500 daga wajen masu garkuwar.
A makon jiya ne masu garkuwar suka sako mahaifiyar Dauda Kahutu bayan ta shafe kwana 20 a hannunsu.