Kannywood
Innah lillahi wa’innah Alaihi Raju’un : Allah yayiwa Mahaifin Jaruma Maimuna Wata Yarinya Rasuwa
Innah lillahi wa’innah Alaihi Raju’un : Allah yayiwa Mahaifin Jaruma Maimuna Wata Yarinya Rasuwa
ALLAH ya yi wa mahaifin fitacciyar jaruma Maimuna Mohammed (Watayarinya) rasuwa a ranar juma’a
Jarumar ta tabbatar wa da mujallar Fim cewa mahaifin nata, Alhaji Muhammad Hameed, ya rasu ne a yau a Kano bayan sallar Azahar.
Shekarun sa 60 a duniya.
An yi masa jana’iza a unguwar su Maimuna ɗin, wato Tishama.
Maimuna ta ce Alhaji ya yi fama da rashin lafiya, inda ta yi jinyar sa na wani lokaci.
Allah ya jiƙan sa, amin.