Kannywood

Inna Sami Mijin Aure Kawai Zanyi -Inji Rayya Kwana Casain

Matashiyar Jarumar nan akannywood, Surayya Aminu wacce aka fi sani da Rayya kwana casain, ta ce a kasuwa take

Ta fadi cewa, a shirye take ga duk mai kaunarta tsakani da Allah

Sananniyar matashiyar jarumar fina-finan Hausa mai suna Surayya Aminu, wacce aka fi sani da Rayya, ta bayyana cewa a kasuwa take don kuwa neman mijin aure take.

Jaruma Rayya ta bayyana cewa, a shirye take ga duk wanda yake so da kaunarta tsakani da Allah zai aureta.

Jarumar ta kara da cewa, shi aure lokaci ne, tana sa ran tayi aure nan ba da dadewa ba cikin ikon Allah.

Idan ba zaku manta ba, a kwanakin baya da Rayya tayi hira da Dala FM a kan abokin aikinta Yawale, jarumar ta ce ba zata iya aurenshi ba saboda yana da mata. Hakazalika, Yawale bashi da makuden kudin da zata iya aurenshi, saboda ita dai mai kudi take so.

Amma daga bisani, jaruma Rayya ta sanar da janye wannan kalaman a shafinta na Instagram.

One Comment

  1. I swear to God if u are ready to married me I’m ready to married her I have a house I’m a business man take my phone number if u are ready please call me to this number 09011604594 or 08091673561

Back to top button
error: Content is protected !!