Labarai

INEC Tayi Amai Ta Lashe Kan Hukuncin Zaben Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta janye wasikar ta ta farko da ke nuna daukaka kara kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 6 ga watan Oktoba mai dauke da sa hannun Suleiman Alkali, shugaban sashin shari’a na hukumar a Kano, INEC ta ce ta janye karar da ta shigar saboda ba ta da dalilin daukaka karar akan duk hukuncin da kotun ta yi.

“Helkwatar hukumar ta umurce ni da cewa INEC a matsayinta, ba ta da wani dalilin daukaka kara a kowane hukunci.”

Idan zaku tuna a ranar 20 ga watan Satumba, kwamitin alkalan kotun mai mutum 3 ya sauke Gwamna Abba Yusuf tare da ayyana dan takarar jam’iyyar APC Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Back to top button
error: Content is protected !!