Kannywood

Ina so na zama ‘yar kasuwa kamar Dangote –Sadiya Kabala

Jarumar fina-finan Hausa Sadiya Kabala ta bayyana cewa burinta shi ne ta zama ‘yar kasuwa mai kudi kamar Alhaji Aliko Dangote.

Sadiya Kabala ta wallafa a shafinta na Instagram cewa ”Mafarki na shi ne in zama ‘yar kasuwa kamar Dangote nima wata kila a kirani ‘Yargote”
Wannan batu na jurumar dai ya sanya cecekuce tsakanin mabiyanta, wadanda suka rika bayyana mabam-bamtan ra’ayoyi akai, yayin da wasu ke mata fatan alkhairi, wasu kuwa tuni ma suka fara kiranta da ‘Yargote.

Wannan dai ba shi ne karon farko da jaruman masana’antar Kannywood ke fatan zamowa ‘yan kasuwa ba, domin kuwa ko a baya-bayan nan matashiyar jaruma Maryam Yahya ta bude shagon kasuwanci a Kano.

Haka kuma ko a makon da ya gabata a wata tattaunawa da jarumi Ali Nuhu yayi da sashen hausa na BBC ya bayyana cewar shi ma yana hadawa da wasu sana’o’in baya ga harkar sa ta wasan kwaikwayo.

Back to top button
error: Content is protected !!