Kannywood

Ina Nadamar Tsinewa Kaina A Fim – Musa Mai Sana’a

Fitaccen jarumin barkwanci a fina-finan Hausa na Kannywood, Musa Mai Sana’a, ya ce yana matukar nadama a game da tsinewa ko la’antar kansa da yake yi a cikin wasu fina-finan da ya fito.

 

A cikin wata tattaunawa da BBC ta Instagram, Mai Sana’a ya ce a da ya yi hakan saboda rashin kwarewa.

Amma a hankali- a hankali sai ya fahimci cewa wannan abu da ya ke fa ba abune mai kyau ba.

 

Ya ce “Da farko-farkon fina-finai na na yi ta yin abubuwa wadanda ni a ganina dai-dai ne, amma daga bisani bayan da wasu mutane suka ja hankalina a kan abubuwan musamman zagi ko tsinewa kaina da nake, sai na fahimci cewa lallai yakamata na daina”.

Musa Mai Sana’a ya ce a yanzu ya kara fahimtar abubuwa a fina-finan hausa na Kannywood, kuma ga girma ma da yazo.

Don haka dole wasu abubuwa a jingine su a daina, musamman da ya ke ga shi an fara tara iyali dole a daina wasu abubuwan a cikin fina-finai, in ji jarumin.

 

Kauce wa Instagram, 1

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1

Mai Sana’a ya ce, shi a fina-finansa ana gani kamar yana wuce gona da iri, to sam shi ya ba ya haka.

 

Ya ce, “Ina yin fina-finai na ne domin nishadi da kuma fadakarwa, kuma na fi yin fina-finai ne ma a kan batun da ya shafi iyaye da ‘ya’yansu”.

Duk abin da aka nayi a cikn fim to fadakarwa nake domin masu irin wannan hali da na yi a ciki fim su dauki darasi su daina inji Mai Sana’a.

@BBCHausa

Back to top button
error: Content is protected !!