LabaraiUngategored

Ina Da Tabbacin Buhari Zai Cika Alkawuran Da Ya Daukarwa ‘Yan Nijeriya, Cewar Janar Babangida

Ina Da Tabbacin Buhari Zai Cika Alkawuran Da Ya Daukarwa ‘Yan Nijeriya, Cewar Janar Babangida

Daga Haji Shehu
Tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bada tabbacin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo karshen matsalar tsaron dake cigaba da addabar Nijeriya.

Da yake ganawa da manema labaru a gidan sa dake Minna ranar Talata, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewar, Shugaba Buhari yana da kwarewar da zai magance matsalolin Najeriya, sannan ya yi kira ga yan Najeriya da su kasance masu hakuri ga shugaban kasar.

Jaridar Daily Trust ta nakalto Babangida yana horon yan Najeriya da su kasance masu hadin kai tare da yiwa shugaban kasa uzuri domin cigaban kasa, sannan ya bada tabbacin cewar shugaba Buhari mutum ne mai alkawari kuma yana da tabbacin zai cika alkawuran da ya dauka musamman akan sha’anin tsaron kasarnan.

Back to top button
error: Content is protected !!