E News

Hotunan Shugaban Kasan Nigeria Tinubu Wajen Tafsir

Tinubu Ya ce A Dage Da Addua’a Don Kawo Karshen Matsalolin Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya bi sahun Musulmai a masallacin gidan gwamnati domin gudanar da tafsirin watan Ramadan a ranar Talata, inda yayi kira ga ‘yan Nijeriya dasu yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

A jawabinsa na bude Tafsiri na shekara-shekara, Shugaba Tinubu ya shawarci al’ummar Musulmi da su rika kyautata wa juna da makwabta, tare da tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma.

“Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya bamu damar ganin watan Ramadan mai alfarma, ya kuma ba mu damar zama ‘yan Nijeriya duk da kalubalen da muke fuskanta, duk da cewa lokaci yana da wahala, amma Allah ya kaddara mana sadaukarwa, mu horas da kanmu, mu taimaki junan Mu in ji Shugaba Tinubu.

Shugaba Tinubu ya tunatar da Malamai irin rawar da suke takawa a matsayin malamai, inda ya jaddada muhimmancin koyar da gafara, hakuri da juriya.

“Ya zama wajibi a kanmu mu sadaukar da duk wani dan abin da muke da shi ga ‘yan’uwanmu, mu kasance masu tausasawa da tawali’u.

Back to top button
error: Content is protected !!