Hotunan Jaruma Halima Atete Tare Da Angonta
MashaAllah! Jaruma Halima Atete Zata Amarce, Kalli Hotunan Kafin Aure Tare Da Angon Nata.
Halima Atete Za Ta Shiga Daga Ciki👰
Tauraruwar Kannywood Haleema Atete da Angonta Mohammed Mohammed Kala Wadanda Za A Daura Aurensu Ranar Asabar 26 ga watan Nuwamban 2022 A Garin Maiduguri.
Jarumar Dai Jaruma Ce Data Shafe Shekaru Da Dama A Masana’antar Na KannyWood, Wanda Asalinta Yar Garin Maduguri Ne,
A Kwanakin Baya Anyi Wani Hasashe Da Yake Nuna Cewa Kamar Duka Masana’antar KannyWood Babu Mace Da Takai Jarumar Kudade. Jarumar Dai Ta Hannun Dama Ce A Wajen Fitacciyar Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya Wacce Itama Ta Shiga Daga Ciki.
Yanzun Kenan Zamu Iya Cewa Jaruman KannyWood Mata Musanman Ma Wanda Su Dan Kwana Biyu A HarKar Sunata Shiga Daga Ciki. Domin A Wannan Shekarar Da Muke Ciki Jarumai Mata Wanda Suyi Aure Suna Da Yawa.
Inda Su Hada Da. Aisha Aliyu Tsamiya, Hafsat Idris Barauniya, Ummi Rahab, Amiran Danda, Rukayya Dawayya, Hassana Muhammad, Da Dai Sauransu.
Allah Ya Sanya Alheri Ya Kuma Basu Zaman Lafiya Mai Daurewa. Amin Summa Amin.







