Kannywood

Hotunan fitsara: Martanin Rahama Sadau Ga Kungiyar kannywood Ni Ba ‘Yar Kano Bace

Shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai, ya ce matsalar da suke fuskanta game da daukar mataki kan jarumar nan ta

masana’antar Kannywood Rahma Sadau cikin wani yanayi marar kyan gani abin kyama ita ce jarumar ta yi ikirarin cewa ita fa ba ‘yar Kano bace saboda haka ba su da iko akanta.freedomfm
Sai dai ya ce kungiyar za ta ci gaba da sa ido kan jarumar domin gano gaskiyar ikirarin da ta yi.

“Matukar muka gano cewa tana karkashin ikon mu ba zamu bata lokaci ba wajen daukar matakin ladaftarwa akanta”
“Ba zamu saurara mata Ina tabbatar muku matukar ta yi kokarin shirya film a yankin da muke iko wato nan jihar Kano.

“Amma a yanzu bamu da iko saboda bazan iya yin hukunci a wata jiha ba saboda suma da nasu shugaban cin”
wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewar,sShugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewar reshen jihar Kano, ya bayyana hakan ne a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a yau Lahadi goma sha biyar ga watan Disamba.

A baya-bayan nan ne dai wasu hotuna da faifan bidiyo da su ka yi ta yawo a kafafen sada zumunta na Facebook da Instagram, aka hango jarumar cikin wani yanayi shiga marar kyan gani na rashin da’a tana ta taka rawa, inda wani sassa na jikinta musamman ta kafarta duk a waje yake.

Back to top button
error: Content is protected !!