Kannywood
Hotunan Aisha Najamu Tare Da Mahaifiyarta
Kyawawan Hotunan Jarumar KannyWood Aisha Najamu (Hajiya Izza) Tare Da Mahaifiyarsa. Jaruma Aisha Najamu Ta Saki Zafafan Hotunan Ne A Shafukan Sada Zumunta Inda Tayi Hotunan Tare Da Mahaifiyarta.
Aisha Najamu Dai Tana Daya Daga Cikin Jaruman Da Tauraruwar Su Ta Haska A Masana’antar KannyWood Musanman Ma A Baya Bayan Nan.
Jarumar Bata Dade Sosai A Harkar Fina Finan Hausar Ba. Inda Zamu Iya Cewa Shirin Izzar So Shiri Mai Dogon Zango Shine Yayi Sanadiyyar Sanuwarta A Idon Duniya.
Jarumar Dai Kamar Yadda Ta Bayyana Ta Tabayin Aure Inda Allah Ya Albarkaceta Da Yara Maza Guda Biyu, Ga Hotunan Nata Tare Da Na Magabaciyar Nata Anan.








