Ungategored

(Hotuna(BABBAN KAMU: DCP Abba Kyari Ya Sake Kama Masu Fashi Da Garkuwa Da Mutane Da Sauran Manyan Laifuka Su Sama Da 70

BABBAN KAMU: DCP Abba Kyari Ya Sake Kama Masu Fashi Da Garkuwa Da Mutane Da Sauran Manyan Laifuka Su Sama Da 70
Daga Datti Assalafiy
Sarkin Yakin Nigeria, Ajalin masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda, DCP Abba Kyari babban kwamandan rundinar IGP Intelligence Response Team (IRT) ya samu nasaran kama wasu rikakkun ‘yan ta’adda mutum saba’in da biyu (72).

Cikin wadannan ‘yan ta’adda saba’in da biyu (72) akwai masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, masu satar mota, masu sata a gurin akwatin cire kudi (ATM Machine), masu safarar miyagun kwayoyi zuwa ga ‘yan ta’adda,
masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami da sauran miyagun mutane masu aikata munanan laifuka.

An samu bindigogi kirar AK47 da harsashin bindiga masu tarin yawa a hannun ‘yan ta’addan, da na’urorin da ake amfani dasu wajen gano location din mutumin da akeso a kama (Tracking Devices), sai kayan tsafi da sihiri, sai miyagun kwayoyi da sauran abubuwa.

‘Yan ta’addan da ake zargi duk sun amince da laifukan da suka aikata, da zaran an kammala bincike za’a gurfanar da su gaban kuliya don su fuskanci hukunci daidai da laifin da suka aikata, sannan ana kokarin kamo sauran abokan ayyukansu na ta’addanci
Jinjina ga Maigirma shugaban rundinar ‘yan sandan Nijeriya IGP Muhammad Abubakar Adamu, jinjina ga Sarkin Yakin Nijeriya DCP Abba Kyari da jama’arsa irin su Bush to Bush Commander ASP Abdurrahman Muhammad Ejily.

Muna rokon Allah Ya kare mana DCP Abba Kyari, Ya tabbatar masa da nasara akan ‘yan ta’adda Amin

Back to top button
error: Content is protected !!