Kalli Hadiza Gabon a dakin Ajiye kayan tarihi na Real Madrid kusa da kofunan Champions League
Tauraruwar fina-finan Hausa wadda itace ta fi shara a shafin Google a shekarar 2019, Hadiza Gabon kenan a wannan hoton nata data dauka a dakin Ajiye kayan Tarihi na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Sifaniya.
Hadiza ta saka kayataccen hoton ne a shafinta na Sada zumunta inda kuma da dama daga cikin mabiyanta suka yaba.
Hadizar tana tsayene a kusa da kofunan Champions League dake ajiye a dakin Tarihin na Kungiyar data lashe a baya.