Labarai
Hotunan Diyar Sarkin Kano tana gaisawa da Osibanjo ya jawo Cece-Kuce
Hotunan diyar sarkin Kano, Khadija Sanusi tana gaisawa da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a yayin da mahaifin nata ke gabatar da ita ga Osinbajon ya jawo cece-kuce a shafukan sads zumunta.
Saidai Khadija ta mayar da martani inda tace ita dai tana son shiga Aljannah. Wani ya saka hotonta tana gaisawa da mataimakin shugaban kasa kuma mutane nata zaginta. Ta kara da cewa ka yi tunanin mutum yaje lahira be shiga Aljannah ba saboda ya bata lokacinshi a Duniya yana gulmar mutane maimakon ibada.