Kannywood

Hira Da Maryam Malika Inda Ta Bayyana Yadda Ayi Ta Dawo KannyWood Bayan Mutuwar Aurenta..

 

Anyi Hirar Ne Tsakanin Hadiza Gabon Da Bakuwarta Wato Maryam Muhammad Malika, Wanda Yanzun Ake Kira Da Mero, Maryam Malika Ta Bayyanawa Duniya Wasu Zarge Zarge Da Akeyi Akanta Inda Ta Qaryata Su.

Da Farko Dai Mai Gabatarwa (Hadiza Gabon) Ta Fara Da Tambayar Maryam Malikan Kan Yadda Ya Taga Masana’antar KannyWood Inda Take Kafin Ta Tafi Tayi Aure Da Kuma Yanda Ta Dawo Ta Tarar Da Industry, Sai Bakuwar (Maryam Malika) Ta Bayyana Cewa An Sami Banbance Da Daman Gaske Musanman Ma Yanda Yanzun Ake Da Kayan Aiki Masu Kyau Fiye Dana Baya. Ta Kara Da Cewa Hatta Yadda Ake Tsarawa Ya Banbanta Da Na Baya,

Sai Hadiza Gabon Din Ta Tambayeta Shin Ya Yanayin Daukakarta Kafin Ta Tafi Tayi Aure Da Kuma Dawowarta.??

Sai Maryam Din Ta Bayyana Cewa Alhamdulillah! Har Yanzun Tana Da Masoya Kamar Yadda Ta Sami Masoya A Baya Kafin Tayi Aure.

Inda Tace Da A Baya Iya Manya Magidanta Ne Kawai Su Santa, Amma Yanzun Kuma Har Qananan Yara Ma Duk Sun Santa, Don Ko Fita Tayi Zataji Anata Kiran Sunanta.

An Tambayi Maryam Din Shin Ko Me Yayi Sanadiyyar Mutuwar Auren Nata, Kuma Shin Tana Son Mijin Nata Har Yanzun.

Bugu Da Kari Hadiza Gabon Din Kara Da Tambayar Maryam Din Wai Shin Dagaske Ne Abin Da Ake Cewa A Kotu A Raba Auren Nata Da Mijinta, Sai Maryam Din Taki Bada Amsa Tace Abar Wannan Maganar Kawai.

Mai Gabatarwa (Hadiza Gabon) Ta Tambaye Maryam Din Shin Menene GasKiyar Fada Da Tayi Da Producers Na Masana’antar KannyWood Kafin Tafiyar Auren Nata, Maryam Din Ta Bayyana Hakan A Matsayin Rashin Fahimta Na Mutane,

Inda Tace Koma An Sami Matsalar, Dama Zo Mu Zauna Ne Zo Mu Saba, Kuma Harshe Da Hakorina Ai Na Samun Matsala Wani Lokaci.

Ana Yawan Cewa Yan KannyWood Sunayin Aure Daga Baya Kuma Su Kashe Auren Su Dawo Domin Suci Gaba Da Harkarsu Ta Shirya Fim. Shine Kema Kin Kashe Aurenki Ne Domin Ki Dawo Ki Daura Daga Inda Ki Tsaya. ??? 

Sai Maryam Ta Bayyana Cewa Ita Sam Bata Da Wannan Niyyar A Ranta, Kuma Bata Taba Wannan Tunanin Ba, Don Haka Tayi Aure Ne A Lokacin Da Allah Ya Kaddara Mata. Sannan Auren Ya Mutu Ne Saboda Haka Allah Ya Kaddara Mata.

An Sake Tambayarta Shin Wanene Abdul M Shareef A Wajenta, Sai Ta Bayyana Cewa Abdul Oganta Ne Kawai A Wajen Aiki, Bayan Nan Babu Wata Alaqa A Tsakani.

Shin Idan Zaki Sake Yin Aure, Akwai Wani Abu Da Zakiyi La’akari Dashi Kafin Ki Sake Wani Auren??

Eh Toh, Duk Wanda Ya Sake Zuwa Wajena Yana Son Aurena Zan Zauna Ne Nayi La’akari Kan Cewa Shin Maryam Malika Zai Aura, Ko Kuma Maryam Muhammad Zai Aura.

Idan Zaki Bar Masana’antar KannyWood Wace Irin Sallama Zaki Musu??

Wannan Karon Babbar Sallama Zan Musu, Inda Hadiza Gabon Cikin Barkwancin Tace Ai Wancan Karon Ma Babbar Sallama Kiyi, Sai Maryam Din Cikin Dariya Tace Wancan Karon Auren Yarinta Tayi. Yanzun Kuma Auren Hankali Zatayi.

Mutane Da Dama A Wancan Lokacin Suna Miki Kallon Mai Girman Kai, Da Kuma Izza Me Zakice Musu???

Eh Toh GasKiya Mutane Da Dama Sunamin Wannan Kallon. Kuma Wannan Abun Ya Samo Asali Ne Tun Daga Fim Din Malika, Inda A Hadani Da Nafisa Abdullahi Da Kuma Ali Nuhu, Inda Aga Ina Rashin Kunya Da Nuna Izza Toh Shiyasa Mutane Ke Tunanin Haka. Amma Maryam Ba Haka Halinta Na Zahiri Yake Ba.

Nan Itama Maryam Malika Tayi Tambayarta Zuwa Ga Mai Gabatarwa, (Hadiza Gabon) Inta Take Tambayarta, Na Shigo Harkar Fim Na Tarar Dake Sannan Naje Nayi Aure Na Sake Dawowa Still Kinanan.

Sai Hadiza Gabon Din Ta Bayyana Cewa Aure Nufi Ne Na Allah, Sai Lokaci Yayi Mutum Zaiyi Shi.

Nan Ne Hirar Tasu Tazo Karshe.. Zamuci Gaba Da Kawo Muku Yadda Take Kasancewa A Gabon Talk Show Dama Wasu Bangarori Na Daban.

Kalli Cikakken Bidiyon Hirar Ana. 

BIDIYON HIRA MARYAM MALIKA DA HADIZA GABON

 

 

2 Comments

Back to top button
error: Content is protected !!