Hira Da Fiddausi Yahaya Wato Zainab Labarina
Inajin Dadi Sosai Yadda Masoyana Su Nunamin Damuwa Kan Kasheni Da Ayi A Shirin Labarina Series – Fiddausi Yahaya. Wato Zainab Labarina Daga Bakin Mai Ita.
Sabuwar Jarumar Dai Da Alamu Ta Shigo Masana’antar Ta KannyWood Da Kafar Dama. Yanda Zamuce Zuwa Yanzun Har Ta Jawo Dumbin Masoya Sosai.
Malam Aminu Saira Dai Ya Lasawa Mutane Zuma A Bakinsu Kuma Yazo Ya Hanasu. Inda Yayi Bazatar Shigo Da Wannan Sabuwar Fuskar Jarumar A Shirin Nashi Na Labarina. Inda Zuwan Nata Duk Da Ba Wani Nunata Ayi Sosai Ba. Har Ta Kwashi Masoya Da Yawa Daga Yan Kallo.
Sai Dai Duk Da An Nuna Cewa Zainab Din Ta Mutu A Cikin Shirin Na Labarina Hakan Baisa An Dan Daina Haskota Ba Kamar Yadda Masoyan Nata Suke Fata. Domin Ana Haskata Jifa Jifa Tana Fitowa A Matsayin Tunani Ko Kuma Labari.
Shafin BBCHausa, Sunyi Hira Da Sabuwar Jarumar A Shirin Nan Nasu Na Daga Bakin Mai Ita, Inda Jarumar Ta Nuna Jin Dadinta Sosai Ganin Yadda Masoya Su Damu Da Ita. Duk Da Ba Wani Jimawa Tayi Da Shigowa Shirin Ba.
Ga Cikakken Hirar Da Ayi Da Jaruma Fiddausi Yahaya Wato Zainab Matar Al – Amin A Cikin Shirin Na Labarina.