Labarai
Har Yanzu Daurawa Ne Shugaban Hisbah- Jam’iyyar NNPP
Har Yanzun Sheikh Daurawa Ne Shugaban Hukumar HISBAH Na Jihar Kano! Martanin Jam’iyyar NNPP Kan Murabus Din Da Shugaban HISBAH Yayi!!
Jam’iyyar NNPP Me Cin Mulki A Jihar Kano, Tayi Martani Kan Murabus Din Da Shugaban Hukumar Hisbah Yayi Kan Mukamin Shugabancin Hukumar.
Hakan Na Biyo Bayan Yadda Gwamnar Jihar Kanon Ya Fito A Bayyanawa Duniya Cewa Bayajin Dadin Yadda Hukumar Ke Tafiyar Da Aikinta.
Wannan Na Daya Daga Cikin Dalilin Da Yasa Babban Malamin Yayi Mmurabus Kan Kujerar Tashi, Inda Mutanen Ciki Da Wajen Jihar Kano Ke Kokawa Kan Wannan Lamarin. Inda Wannan Dalilin Ya Fara Jawowa Gwamnatin Jihar Kanon Baqin Jini, Inda Mutane Ke Ganin Gwamnan Ya Zabi Mutanen Banza Kan Na Arziki.
Ga Abin Da Jam’iyyar NNPP Din Ke Cewa.