E News

Hankalin Yan Tiktok Ya Tashi Bayan Sunji Za.a Kulle

Yadda Hankalin Yan Tiktok Ya Tashi, Bayan Sunji Labarin Saura Kwana Uku A Kullu Tiktok, Ananan Ana Ci Gaba Da Muhawara A Shafin Tiktok, Inda Labari Yazo Daga Majiya Mai Karfi Cewa Anaso A Toshe Shafin Tiktok Gaba Daya.

A Yanda Labarin Yake Zuwa Shine, Amurka Ce Take So A Cire Tiktok Din Daga Shafin PlayStore Da Kuma App Store, Saboda Su Amurka Suna Kishi Kan Cewa Shafin Tiktok Din Ya Kwacewa Facebook Da Tiwita Mutane,

Kamfanin Tiktok Kamfani Ne Na Dan China, Wanda Shi Kuma Ya Samu Karbuwa Cikin Lokaci Kalilan, Hakan Yasa Sauran Masu Shafukan Sada Zumunta Musanman Ma Na Amurka Suke Kishi Ko Muce Hassada Akan Hakan.

Dama Kuma Tun Kafin Yanzun Amurka Suna Takun Saqa Da Duk Wani Kaya Na China, Da Zai Iya Kwashe Kasuwar Kayansu Na Amurka, Ma Iya Cewa Su Amurka Suna So Ya Zama Komai Na Duniya Nasu Ne Akan Gaba,

Zuwa Yanzun Hankulan Mutane Da Dama Musanman Yan Arewa Tiktok Ya Tashi Sakamakon Nan Ne Wajen Nishadinsu, Inda Zuwa Yanzun Wasu Har Sunyi Ban Kwana Da Shafin Na Tiktok.

Mun Kawo Muku Bidiyo Yadda Hankalin Yan Tiktok Din Ya Tashi Bayan Sunji Labarin Kulle Tiktok Din.

https://m.youtube.com/watch?v=-0jFkq-YSz0

 

Back to top button