Kannywood

Halisa Muhammad Na Neman Taimako Kan Cutar Da take Fama Dashi

Abin Da Ya Sa Tsohuwar Jarumar Kannywood Halisa Muhammad Take Neman Taimakon Kan Lalurar Da Take Fama Dashi.

Tsohuwar Jarumar A Masana’antar Kannywood, Hajiya Halisa Muhammad ta na neman taimakon al’umma da su taimaka mata da kuɗi ko kuma saya mata allura da za a riƙa yi mata saboda jinyar da ta ke fama da ita ta sankarar mama (breast cancer).

Halisa Muhammad

Allurar za a yi mata ita ce har sau goma sha takwas, kuma duk ƙwaya ɗaya kuɗin ta ya kai N335,000.

An ga jarumar cikin wani bidiyo a soshiyal midiya inda ta ke neman taimako da kan ta. A ciki ta na cewa, “Assalamu alaikum wa rahamatullah. Suna na Halisa Muhammad. Ni ce mai fama da ciwon ‘breast cancer’, wato kansar mama kenan, na ke neman muhimmin taimako a wurin ku bayin Allah na wata muhimmiyar allura, kuma kuɗin ta na da tsada sosai, na ke neman taimakon ta a wurin ku bayin Allah.

“Allurar ta kan kai N335,000 duk ƙwara ɗaya. Kuma allurar nan za a yi ta sau goma sha takwas; round goma sha takwas za a yi min ita.

“‘yan’uwa da abokan arziki sun yi bakin ƙoƙarin su a kan ciwon nan. Kansa na da wahalar sha’ani, shi ya sa na fito na nemi taimakon ku, bayin Allah, ku ma ku taimaka min da kuɗin allurar nan ko allurar, kuma ina barar addu’o’i.

“Ubangiji Allah ya ba mu lafiya, ya kuma ba da ikon taimakawa.

“Zan aje akawun lamba ɗi na da kuma lambobin wayoyi na, duk wanda Allah ya ba shi iko ya taimaka mana da kuɗin allurar ko allurar. Allah ya ba ku iko, na gode sosai.”

Halisa ta ɗauki tsawon lokaci ta na fama da wannan jinya, wanda har ta kai ga a watannin baya abokan sana’ar ta ‘yan fim sun tara mata kuɗi don fitar da ita ƙasar waje neman magani.

Kuɗin bai kai adadin da ake nema ba, don haka dole sai a gida aka yi mata aikin a wani asibiti a cikin garin Kano.

Tun a shekarar da ta gabata mujallar Fim ta so ta tattauna da ita a kan rashin lafiyar, sai dai kuma ita Halisar ta ƙi amincewa, ta roƙe mu da kada ma mu ba da labarin halin da ta ke ciki.

Sai dai a kwanan baya mun ba ku labarin ziyarar da wasu daga cikin abokan sana’ar ta su ka kai mata, wato ‘yan guruf ɗin Kannywood Family, a ƙarƙashin jagorancin tsohuwar jaruma Hajiya Hindatu Bashir da su mawaƙi Muddassir Ƙassim.

Bayan tura bidiyon neman taimakon da Nura Mado ya yi a cikin guruf ɗin, da dama sun tofa albarkacin bakin su a kan cewa ya kamata waɗanda su ka samu dama a cikin gwamnatin Kano irin su Abba El-Mustapha, Sanusi Oscar 442 da Fauziyya D. Sulaiman su taimaka su yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf magana ko za a dace.

Daga baya ita Halisar ta tura wani saƙo a Facebook da kuma cikin guruf ɗin da cewa, “Alhamdu lillah, mu na ganin ƙauna”. Sannan ta rubuta, “Allah ya saka da gidan Aljanna, Allah ya sa a mizani.”

Halisa Muhammad

Ga dukkan wanda ke son ba da nasa taimakon, ga lambar asusun ta na banki:

Lambar asusu: 0006710251

Banki: Jaiz Bank.

Suna: Halisa Muhammad Abdullahi

Allah ya sa a dace, amin.

Daga Shafin Fimmagazine.com

Back to top button
error: Content is protected !!