Kannywood
Halima Atete Da Angonta Ana Shan Soyayya
MashaAllah! Bayan An Kammala Shagulgulan Biki, Amarya Halima Atete Da Angonta Suna Shan Soyayya, An Bayyana Wasu Hotuna Na Tsohuwar Jarumar Halima Atete Tare Da Angon Nata Inda Sukema Mutanen Dasu Halarci Bikin Nasu Ban Gajiya.
A Ranar Asabar Daidai Da 26 Ga Watan 11 Ne Aka Daura Auren Na Jaruma Halima Atete Da Angonta Muhammad Muhammad Kala. Bikin Nasu Ya Sami Halartar Manya Da Kananan Jaruman KannyWood. Inda Asha Shagali Kala Kala.
Bayan Kammala Shagulgulan Ne Sai Akaga Wasu Hotunan Amarya Tare Da Angon Nata Suna Cin Amarcinsu.
Muna Musu Fatan Alkairi Tare Da Addu’ar Allah Yasanya Albarka A Cikin Tarayyar Tasu. Allah Kuma Ya Aurar Da Yan Baya Lafiya. Amin Summa Amin.