Hajiya Rabi Bawa Mai Kada (Rahama Mk) Ta Haihu
Hajiya Rabi Bawa Mai Kada Jarumar Fina Finan KannyWood (Rahama MK) Ta Cikin Shirin Kwana Casa’in Ta Haihu Na GasKe Bana Fim Ba.

Jiya Ne Muke Samun Labarin Haihuwar Jarumar. Inda Ta Haihu Cikin Koshin Lafiya, Sai Dai Da Yawan Mutane Basu San Cewa Jarumar Tana Da Aurenta Ba.
Sai Dai Mu Nan Munsha Kawo Maku Hotunan Jarumar Tare Da Mijinta Wacce Tayi Aure Sama Da Shekaru Biyu Kenan Dasu Gabata.
A Satin Nan Ne Dai A Bayyana Hajiya Rabi Bawa Mai Kada A Matsayin Wacce Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Alfawa Karkashin Jam’iyyar Guguwa Party Inda Ta Kayar Da Abokin Karawarta Na Jam’yyar Haske Wato ABM Adnan, Amma Fa A Cikin Shirin Na Kwana Casa’in 😄
Mansura Isah Tana. Daya Daga Cikin Wanda Su Wallafa Bidiyon Jaririn Da Rahama MK Ta Haifa A Shafin Sada Zumunta, Tare Da Tayata Murnar Haihuwar Abokiyar Aikinta Kuma Wacce Kabilarsu Daya Wato (Yoruba).
Muma Daga Nan Shafin HausaMini.Com.Ng Muna Taya Jarumar Tare Da Maigidanta Murnar Samun Karuwar Haihuwa Da Suyi. Allah Ya Raya Musu Abin Da A Haifa Amin.
BAZAN IYA DAINA FIM BA DUK DA CEWA INA DA AURE
Jaruma Rahama MK, Wacce Akafi Sani Da (Hajiya Rabi Bawa Mai Kada) Ta Bayyana Cewa Mace Zata Iya Ci Gaba Da Yin Fim Koda Tana Da Aure, Kamar Yadda Zata Iya Ci Gaba Da Aikin Banki Ko Koyarwa.
Ta Bayyana Cewa Kafin Aurenta Akwai Yarjejeniyar Cewa Zata Iya Ci Gaba Da Yin Shirin Fim Dinta Koda Tayi Aure, A Watannin Bayane Muka Sami Labarin Jarumar Tayi Auren Sirri, Inda Bayan Auren Nata Kuma Akaci Gaba Da Ganinta A Cikin Shirin Kwana Casa’in Inda Taci Gaba Da Taka Rawa Kamar Yadda Ta Saba.
A Wani Hira Da Shafin BBC Hausa Suyi Da Ita, Ta Bayyana Cewa Ta Tabayin Aure A Garin Jos. Har Tana Da Yara Guda Biyu, Daga Baya Kuma Auren Ya Mutu Ta Koma Kano Nan Ne Kuma Sai Taci Gaba Da Harkokinta Na Fina Finai.
Hajiya Rabi Bawa Mai Kada. Ko Muce Rahama MK, Jigo Ce A Cikin Shirin Na Kwana Casa’in Sannan Zamu Iya Cewa Tana Daya Daga Cikin Gishirin Shirin Saboda Irin Rawar Da Take Takawa.
Jarumar Ta Bayyana Cewa Duk Da Cewa Ita Ba Bahaushiya Bace, Amma Kuma Bata Samun Wani Wariya Ko Nuna Qabilanci A Masana’antar KannyWood, Ana Daukarta Kamar Yadda Ake Daukar Kowace Jaruma.
Yanzun Dai Jarumar Tananan Tare Da Mijinta Cikin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali. Muna Fatan Allah Ya Kara Musu Zaman Lfy Da Kwanciyar Hankali.
Mun Kawo Muku Cikakken Bidiyon Hirar Da Shafin Na BBC Hausa Suyi Da Ita, Inda Zakuji Daga Bakinta, Kuma Kusan Ko Ita Wacece Da Tarihin Rayuwarta.







