Hafsat Shehu Tsohuwar Matar Ahmed S Nuhu, Tayi Aure Bayan Shekaru 13 Da Mutuwar Mijinta
Wani labari da muke samu a yau Juma’ar nan ya bayyana cewa tsohuwar jarumar fina-finan Hausa Hafsat Shehu ta yi aure
Jarumar dai ta kasance tsohuwar mata ga marigayi jarumi Ahmad S Nuhu
Jarumar dai tayi aure na bazata ne, inda ta yi kokarin ta boye ango da ranar auren nata, amma daga baya anji ‘yan uwa da abokan arziki suna yi mata murna
A wani labari da Tashar Tsakar Gida ta YouTube ta wallafa ta bayyana cewa a yau Juma’ar nan ne aka daura auren jaruma Hafsat Shehu wacce ta kasance tsohuwar matar ga marigayi jarumi Ahmad S Nuhu, haka kuma ta kasance tsohuwar jaruma a masana’antar Kannywood.
Duk da dai bayan rasuwar mijin nata an bayyana cewa tayi wani auren a Abuja, amma kuma Allah bai sa auren ya dore ba. A wata majiyar tun bayan mutuwar auren nata ta so dawowa harkar fim amma mashawarta suka hanata.
Sai dai a ‘yan kwanakin nan jarumar ta tabbatar da dawowar ta harkar fim din inda har jarumi Adam A Zango ya wallafa hoton sabon fim din da ya sanya ta a ciki mai suna ‘Basaja Sabon Labari’ wanda har ya zuwa yanzu dai ba a kai ga fara dauka ba sai wasu rigimu suka kunno kai ga jarumin Adam A Zango ta bangaren hukumar tace fina-finai da kuma malaman addini.
Ga dukkan alamu Hafsat Shehu tayi irin auren da mafi yawancin jaruman Kannywood kanyi ne ma’ana a boye ango kuma a boye ranar auren wanda hakan ce ta faru sai ji aka yi ‘yan’uwa da abokan arziki na mata fatan samun zaman lafiya a gidan mijinta.
Haka muma muna yi mata fatan Allah ya bata zaman lafiya da zuri’a dayyiba.