Kannywood

Hafsat Idris Tayi Magana Akan Aurenta

Fitacciyar tauraruwar fina-finan Kannywood, Hafsat Idris, ta musanta rade-radin da ake yi cewa ta auri daya daga cikin ‘ya’yan tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha.

Ta bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinta na Instagram, ko da yake ba ta bayyana mutumin da ta aura ba.

Hafsat Idris, wadda ake yi wa lakabi da ‘Hafsat Barauniya’ ta yi aure a asrice a karshen makon jiya, lamarin da ya sa wasu kafafen watsa labarai suka bayar da rahotannin cewa ta auri daya daga cikin ‘ya’yan marigayi Janar Abacha.

Amma a sakon da ta fitar domin mika godiya ga mutanen da suka yi mata fatan alheri, tauraruwar ta ce “ina mika sakon godiyana ga dukkan masoya, ‘yan uwa da abokan arziki na fatan alheri da suka yi mini.

Sai dai ina so na yi na yi magana a kan rade-radin da ke yawo…cewa mijin da na aura yana da alaka da gidan Abacha. to, wannan ba gaskiya ba ne.”

Tauraruwar, wadda ke da ‘ya’ya shida gabanin wannan auren nata, ta fito a manyan fina-finai na Kannywood, amma an fi saninta da fim din da ta soma fitowa mai suna ‘Barauniya’.

A kwanakin baya ne babbar ‘yar tauraruwar ta haihu, inda ta yi mata takwara.

 

Back to top button
error: Content is protected !!