Kannywood
Hadiza Gabon Tayiwa Wasu Matasa Goma Ta Arziki
Jarumar Fim, Hadiza Gabon Ta Tallafawa Wasu Matasa Masu Tallar Kosai Da Jari
Jarumar finafinan Hausa, Hadiza Aliyu Gabon ta tallafawa wasu matasa masu sana’ar tuya kosai mazauna Tudun Maliki dake birnin Kano.
Ta ba su tallafin kudi ne domin su habaka jarinsu domin shigaba da tallafawa kansu. Darakta Hassan Giggs da kuma ‘yar jarida Zainab Mohd Abubakar su suka wakilci kai tallafin.