Kannywood

Hadiza Gabon Ce Gwarzuwar Shekarar 2019 A Google

Tauraruwar fina-finan Hausa Hadiza Aliyu Gabon ta shiga cikin jerin taurarin da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-bata na Google a shekarar 2019 a Najeriya, bbchausa.com ta ruwaito.

Taurarin fim din kudancin Najeriya wato Nollywood, Regina Daniels da Genevieve Nnaji da Tonto Dike, su ne kan gaba, yayin da Hadiza Gabon take biye masu a matsayi na hudu.

Shafin Google yakan fitar da kalmomi ko kuma sunayen da mutane suka fi bincikawa a shafin duk shekara a kowace kasa a fadin duniya.

Sannan kuma shafin kan yi wa sunayen rukuni ne, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da ‘yan fim da fina-finan kansu da kuma tambayoyi.

Kamar yadda bayanai suka nuna, Hadiza ta fi yin fice ne daga ranar 7 ga watan Afrilu zuwa 13 ga Afrilun.

A watan Afrilu ne wani bidiyo ya bulla, inda ya nuna Gabon tana dukan Amina Amal bayan Amal din ta zarge ta da yin madigo. kuma wannan ya taimaka wurin kara yawan neman bayanai kan tauraruwar a Google.

Kalmomin da aka fi amfani da su wurin neman karin bayani a kanta su ne: ‘hadiza gabon and amal, hadiza gabon and amina amal, hadiza gabon instagram, tarihin hadiza gabon.’

‘Yan Kano ne suka fi bincika Hadiza Gabon din, inda suke da kashi 100%, sai Kaduna da suke da kashi 63%, sai Abuja masu kashi 52, sai Legas masu 41% da kuma jihar Bayelsa masu kashi 38%.

Wannan na nufin Hadiza gabon ta fi kowane mutum fice a shafin na Google a Arewacin Najeriya ban da Atiku Abubakar, wanda yake na biyu a rukunin mutane a bayan mawaki Naira Marley.

Gabon tana da mabiya miliyan daya da dubu 400 a shafin Instagram, dubu 416 a Facebook da kuma dubu 194 a Twitter.

Back to top button
error: Content is protected !!