Gwarzon Shekara Ya Samu Kyautar 1 Million
Abun A Yaba: Dan Wasan Barkwanci Daga Kasar Igbo Ya Bai Wa Jarumin Yaro Ɗan Barno Mai Dakakkiyar Zuciyar Zangazangar Kyautar Naira Miliyan Guda, Yayi Alƙawarin Sanya Yaran Makarantar Boko
Abun ban sha’awa ne yadda ɗan wasan barkwanci a kafar soshiyal Mediya Ɗan Ƙabilar Ibo mai suna Agozi Samuel, ya nuna bajinta ya bai wa yaron nan Ɗan Barno da hoton zangazangarsa ya karaɗe kafar soshiyal midiya duba da jarumtarsa, kyautar Naira miliyan ɗaya ya kuma yi alƙawarin sanya yaron makarantar boko, ya ce ya yaba da jarumtar yaron, don haka ya ba shi gudunmawa ba tare da la’akari da bambanci addini ko kabila ba, ya ce dukkanmu ‘yan Najeriya ne.
Ga dai abun da Agozi Samuel, ya ce bayan ya tura wa yaron Naira miliyan ɗaya;
“Na cika alkawarin da na yi wa wannan karamin yaro, kuma a karshen mako zan hadu da shi a jihar Barono domin yi masa rijista a makarantar kwana mai zaman kanta.
“Duk da cewa shi ba ɗan kudu maso gabas ba ne, dukkanmu ‘yan Najeriya ne kuma Najeriya ɗaya ce, ɗan haka na ɗauke shi tamkar ɗana kuma zan tabbatar ya samu rayuwa mai kyau.
“Wannan yaro ne marar tsoro a bangaren soja kuma zan tabbatar ya samu ilimi, don haka a karshen makon nan zan je Barno da Kano don haka idan kun kasance masoyana ku bibiyi page dina kuyi following don in albarkace ku da dan abin da nake da shi.
“Yayin da muke addu’ar Allah ya kara wa Najeriya zaman lafiya, muna fatan zamu iya samun sauki, amma mu guji tada husuma ko tarzoma, muyi Zangazangar cikin Lumana” in ji Agozi Samuel.