Labarai

Gwanatin Kano Ta Ragema Asalin Yan Kano Kudin Makaranta

Gwamnatin Jihar KANO Ta Sanar Da Rage Ma  Yan Asalin Jihar Kudin Makaranta Da Kaso 50

Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin gwamnan Abba Kabir Yusuf, ta rage wa ɗalibai ƴan asalin Jihar masu sha’awar fara karatu a manyan makarantun gaba da sakandire mallakin Jihar kuɗin makaranta da kaso 50.

Gwamnatin ta sanar da cewa duk wanda zai shiga makarantar fasaha domin yin karatun HND, zai biya Naira 11,800, wanda kuma yake kan yi zai cigaba zai biya 10,500.

Sannan kuma waɗanda za su fara karatun ND da NCE za su biya Naira 10,275, yayin da waɗanda suke kan yi za su dawo za su biya Naira 9,550. Sai kuma waɗanda za su yi karatun share fagen shiga NCE da ND ɗin su kuma za su biya 10,500.

Back to top button
error: Content is protected !!